Daga Wakilin Mu Suleiman Abubakar MAPSA
Cif Isaac Danladi, babban É—an takarar jam’iyyar APC a zaÉ“en kananan hukumomi da ke tafe a Jihar Nasarawa, ya yi alkawarin farfado da Æ™aramar hukumar Karu idan aka zaÉ“e shi.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan sayen fom ɗin takararsa, tsohon sakataren dindindin ya jaddada cewa ƙaramar hukumar Karu na cikin mawuyacin hali kuma tana buƙatar jagora mai gaskiya da ƙwarewa don dawo da martabarta.
Danladi, wanda yake da Æ™warewa a matsayin babban akawun na ma’aikata, ya tabbatar da cewa yana da kwarewar da ake buÆ™ata don sarrafa kuÉ—aÉ—en da za su shigo Æ™aramar hukumar cikin hikima da nagarta don amfanin al’umma.
Yana da tabbacin cewa zai iya sarrafa dukiyar da ake samu da kyau, yana mai cewa, "Ina da tsari mai kyau da shirin bunkasa Karu."
Danladi ya nuna cewa ci gaban ababen more rayuwa da cigaban bil’adama sune manyan ayyukan da zai fifita idan ya zama shugaban Æ™aramar hukumar.